Jam’iyyar APC ta nada tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu-Shettima a zaben 2027 da ke tafe.
Da take sanar da kafa Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na 2027 a ranar Asabar, APC ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kasance shugaban kwamitin, Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kwamitin mai mambobi 108.
A cikin wata sanarwa a safiyar Asabar, Bayo Onanuga, Mai Magana da Yawun Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana cewa, Shugaban APC na Kasa, Farfesa, Nentawa Yilwatda, zai kasance mataimakin shugaba, a yayin da tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, zai kasance Sakataren kwamitin.
Sakataren APC na Kasa, Sanata Ajibola Bashiru zai kasance Mataimaki Sakataren Kwamitin tare da Hadiza Bala-Usman, a yayin da Abdulaziz Yari ke matsayin Darakta-Janar.
Mataimakan Darakta-Janar sun hada da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril; Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas; Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni; Santa Bamidele Opeyemi.
Yari zai kuma yi aiki tare da sakatarori uku masu kula da yada labarai — Temitope Ajayi, Arabinrin Aderonke, da Frederick Nwabufor. Segun Dada zai kasance Daraktan kafofin yada labarai na zamar, kamar yadda ya yi a 2022, Solomon Arowolo kuma sakataren yada labari da kafofin sada zumunta.
Sanata Adams Oshiomhole shi ne Mataimakin Darakta-Janar mai kula da wayar da kan jama’a a yayin da Shugaban Ma’aikatan Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila ke matsayin Mataimakin Darakta-Janar mai kula da gudanarwa.
Sanata Jamesa Faleke, wanda ya taka muhimmiyar rawa a yakin neman zaben Tinubu a 2022/2023, yanzu shi ne Mataimakin Darakta-Janar mai kula da tsare da da sa ido. Mis Stella Okotete, Injiniya Abdullahi Garba Ramat da Audu Maikori za su kasance sakatarorin sashen tsare-tsaren zabe.
Faleke zai yi aiki da daraktocin yankunan siyasa — Satana Olushola Adeyeye (Kudu maso Yamma), Dakta Ngozi Olejeme (Kudu maso Kudu), Sanata Uche Ekwunife (Kudu maso Gabas), Muntaqha Rabe (Arewa maso Yamma), Ahmed Muhammed Ketso (Arewa ta Tsakiya), da Sanata Sani Danladi (Arewa maso Gabas).
Shahen kula da harkokin shari’a zai kasance Muiz Adeyemi Banire shi a matsayin Darkatan tare da Dakta Liman Hassan da Babatunde Ogala a matsayin matakan darakta. Mambobin su ne Prince Lateef Fagbemi, tsohon Gwamnan Jihar Katsina Ibrahim Shema, Worgu Boms da Dakta Kingsley Tochukwu Udeh.