Tinubu ya yi alhinin rasuwar ɗan kasuwar Kano Bature Abdulaziz

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da jimami kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma jagoran al’ummar ’yan kasuwa a Jihar Kano, Alhaji Bature Abdulaziz, wanda ya rasu a ƙarshen mako.

Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar, Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar ’yan kasuwa a Kano da iyalan marigayin, da gwamnatin Jihar Kano bisa wannan babban rashi.

Shugaban ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ba ga al’ummar kasuwancin Kano kaɗai ba, har ma da sassa da dama na Najeriya, duba da tasirinsa a harkokin kasuwanci.

A cewar Tinubu, marigayi Bature Abdulaziz ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin kasuwanci a ƙasar, inda ya shugabanci ƙungiyoyi da dama masu alaƙa da kasuwanci.

Kafin rasuwarsa, shi ne Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwa ta Najeriya tare da bayar da gudunmawa mai yawa wajen haɗa kan ’yan kasuwa a faɗin ƙasa.

Tinubu ya kuma tuna da irin goyon bayan da marigayin ya ba shi a lokacin yaƙin neman zaɓensa a shekarar 2023, tare da rawar da ya taka wajen inganta haɗin kan ƙasa da kishin ƙasa ta hanyar ƙungiyar Patriotic Elders Network for Peace (PENP) da ya kafa.

Post masu alaƙa

Yar Najeriya ta kammala jami’ar Burtaniya da daraja ta daya (1st Class) a ilimin kimiyar samar da manhajar kasuwancin zamani.

Gwamnati ta buƙaci jama’a su guji taɓa kumfar da ta ɓulla a hanyar Kaduna-Abuja

A riƙa yi wa masu shirin aure gwajin miyagun ƙwayoyi :- Buba Marwa