Home » Trump Ya Yi Alƙawarin Zama Jakadan Zaman Lafiya 

Trump Ya Yi Alƙawarin Zama Jakadan Zaman Lafiya 

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Shugaban Amurka na 47 Donald Trump ya sha alwashin tabbatar da zaman lafiya a duniya yayin rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasar yau Litinin 20 ga Janairun 2025.

Trump ya karɓi rantsuwar kama aiki a sabon wa’adin mulki na shekaru 4 bayan nasarar da ya samu a zaɓen da ya gudana a watan Nuwamban da ya gabata.

A yayin jawabin da ya gabatar a Majalisar Tarayyar Amurka ta Capitol, Trump ya soki manufofi da tsare-tsaren gwamnatin da gabata musamman matakan da ta ɗauka a kan iyakokin ƙasar.

Trump ya nuna ƙiyayyarsa ƙarara ga yaƙe-yaƙen da ake yi a ƙasashe daban-daban na duniya, ya kuma sha alwashin kawo ƙarshensu.

“Amurka za ta tanadi dakaru da ƙasashen duniya za su yi shakka ta yadda duk wani yaƙi da ake fafatawa a duniya zai zo ƙarshe.

“Sannan duk wani yaƙi da bai shafe mu ba ba za mu shiga ba saboda haka zan kasance jakadan zaman lafiya.”

Ya ƙara da cewa, gwamnati da ta gabata ta samar da mafaka ga “manyan masu aikata laifi” waɗanda suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce, “Sabon babin ci gaban Amurka zai fara ne daga yau.

“Daga yau, ƙasarmu za ta fara samun ci gaba kuma za a mutunta a duniya.

“Zan sanya muradun Amurka a gaban komai,” inji Trump.

 

 

 

 

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?