Mazauna da masu sana’ar sayar da abinci a Babban Birnin Tarayya, Abuja, sun bayyana damuwa kan yadda farashin kayan lambu da sauran kayan abinci ke ci gaba da tashi, inda suka koka kan cewar hakan na barazanar wajen ciyar da iyalansu.
Masu sayar da abinci a Abuja sun ce farashin tumatir, barkono, tattasai da sauran kayan miya ya yi tashin gwauron zabi a watannin baya-bayan nan, lamarin da ya tilasta musu sauya yadda suke gudanar da sana’arsu.
Wata mai gidan abinci, Mary Augustine, ta ce babban kwandon tumatir da ake sayarwa tsakanin Naira 45,000 zuwa Naira 48,000 a baya yanzu ya kai kusan Naira 90,000.VVV
Ta kuma ce buhun barkono mai nauyin kilo 50 da ake sayarwa kusan Naira 30,000 yanzu ya har Naira 150,000.
A cewarta, masu sana’ar abinci yanzu suna kashe sama da ninki biyu na kudin da suke kashewa wajen sanyaya a baya, yayin da kwastomomi har yanzu ke son a ci gaba da ba su abinci kan yadda ake ba su a baya.
Ta bayyana cewa domin rage tafks asara, yanzu tana sayen kayan lambu kai-tsaye daga manoma da yawa sannan ta adana domin rage yawan zuwa kasuwa.
Wata mai sana’ar sayar da abinci, Fatima Muhammad, ta ce tsadar tumatir da barkono ya tilasta mata sauya yadda take girki.
Ta ce yanzu tana sayen kayan miya kaɗan-kaɗan tare da amfani da tumatir na gwangwani da barkonon leda.
Ta ƙara da cewa albasa ce kaɗai ba ta yi tsada sosai ba, amma rashin wutar lantarki na sa adana kayan abinci na zama ƙalubale, wanda hakan ke sa kayan lalacewa.
Wata mai sana’ar abincin biki, Lateefat Yusuf, ita ma ta ce tsadar kayan lambu ya shafi sana’arta sosai.
Ta ce kuɗin da take zuwa kasuwa da su yanzu ba sa iya sayen rabin kayan da take saye a baya.
Ta ce masu sana’ar girki da dama na shan wahala wajen ƙoƙarin gamsar da kwastomominsu tare da kaucewa yin asara.
Wasu masu sayar da abinci sun danganta tashin farashin kayan abinci da tsadar sufuri, matsalar tsaro a yankunan noma da kuma asarar kayan gona bayan girbi.
Wani mai gidan abinci, Isah Sagir, ya ce yanzu masu sana’a irin tasu na ƙoƙarin amfani da kayan girki cikin hikima domin kauce wa asara, saboda ƙarin farashin abinci na iya sa su rasa kwastomomi.
Mazauna birnin ma sun koka kan yadda tsadar abinci ke shafar rayuwarsu ta yau da kullum.
Wata matar aure, Maman Zainab, ta ce iyalai da dama yanzu sun koma amfani da busassun kayan lambu da tumatir na gwangwani saboda tsadar kayan marmari.
Wani ma’aikacin gwamnati, Benjamin Amos, ya ce yanzu yana kashe ƙarin kuɗi wajen sayen abinci saboda gidajen abinci sun ƙara farashi.
Wani manomin kayan lambu, Abdulwahab Ishaq, ya danganta matsalar da taɓarɓarewar tattalin arziƙi, rashin tsaro a yankunan noma, matsalolin sufuri da kuma sauyin yanayi da ke shafar noma.
Ya yi kira ga gwamnati da ta tallafa wa manoma, ta inganta hanyoyin sufuri da samar da wuraren adana kayan gona domin rage asarar abinci da kuma sauƙaƙa farashin kayan abinci a faɗin ƙasar nan.