Daga Muhammad Auwal Suleiman da Hauwa Umar Tela
Ƙungiyar tsoffin ‘yan sandan Najeriya (REPON) reshen jihar Bauchi ta bayyana cewa mambobinta guda 500 sun mutu ba a biya su hakkinsu na kammala aiki ba.
Haka zalika REPON ta bayyana rashin jin daɗinta bisa gaza aiwatar da ƙudurin neman a kafa hukumar da zata lura da hakkokin tsofaffin ‘yan sandan Najeriya dake gaban majalisar wakilai tun shekarar 2012.
Waɗannan bayanai na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da sakataren ƙungiyar tsofaffin ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi ASP John Iliya mai ritaya ya yi wa ‘yan jarida.
Ya ce “ mun gaji da gafara sa ba mu ga ƙaho ba, lokaci ya yi da za a ɗauki mataki”
- Matsalar Rashin Tsaro Na Neman Kassara Arewacin Najeriya– Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa
- Ku Miƙa Wuya Ko Ku Ɗanɗana Kuɗar Ku- Gargaɗin Tinubu Ga Ƴanbaindiga
Sakataren ya ce, sun yi zanga-zangar lumana a ƙofar majalisar wakilan Najeriya dake Abuja ranar 21 ga Watan Mayu, 2024.
A lokacin wannan zanga-zangar, shugaban kwamitin harkokin ‘yan sandan Najeriya a zauren majalisar dattawan Najeriya, sanata Ahmed Abdulkadir Malam Madori da wasu abokan aikinsa sun musu alƙawari cewa za a dubi lamarin su a watan Satumba.
Ya ce, har a ranar 2 ga watan Oktoba, ba a taɓa ambaton maganar tsofaffin ‘yan sanda ba a majalisar, musamman ma waɗan da suka fito daga jihar Bauchi.
ASP John Iliya mai ritaya ya ce idan har majalisar bata tuno da su ta yi abin da ya dace ba, to ba shakka za su fito su sake yin zanga-zanga.
Ya ce, ɗaya daga cikin manyan buƙatun da suka gabatar wa majalisar wakilan Najeriya shine fatan a cire ‘yan sandan Najeriya daga tsarin fansho na CPS, a dawo a ƙirƙiri hukuma mai zaman kanta da za ta sa ido akan harkokin haƙƙoƙinsu.
Hakan a cewar sa, zai taimaka wajen bai wa ‘yan sandan dama su lura da haƙƙinsu yadda ya kamata.
REPON ta bayyana rashin jin daɗinta dangane da yadda majalisar ta gaza tattaunawa akan batun da ya shafi tsofaffin ‘yan sandan.
Ƙungiyar ta ƙalubalanci majalisar bisa yadda suka gaggauta sanya hannu akan ƙudurin neman a tsawaita wa shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya shekarun aiki bayan lokacin ritayarsa ta yi. Amma aka manta da buƙatar da suka miƙa.
A ƙarshe sun buƙaci majalisa ta gaggauta duba ƙudurin da suka aika mata, ko kuma a fuskanci mummunar zanga-zanga.