Tsohon Hadimin shugaba Buhari Ya Zama Mataimakin Shugaban Jaridar The Sun

Tsohon Mai Ba Wa Shugaban Ƙasa Shawara a Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Femi Adesina, ya ce, ya shirya karɓar mukamin mataimakin shugaban Jaridar The Sun, wanda ake sa ran zai fara aiki a ranar 1 ga watan Satumba.

A baya dai Femi Adesina ya riƙe muƙamin Edita a Kamfanin Jridar ta The Sun, a matakai daban-daban.

Wannan bayani, ya fito ne daga bakin Adesinan a yayin da yake tattaunawa da manema labarai, Inda ya bayya na cewar, Shugaban Kamfanin, Senator Orji Kalu,  ya tabbatar da ba shi muƙamin.

Adesina ya ce a yayin da ya bayyana aniyarsa ta barin gidan jaridar a baya, Kalu ya shawarce shi a kan kada ya rubuta takardar barin aiki.

A maimakon haka sai ya ba shi damar ya je ya riƙe mukaminsa na Gwamnati, daga baya bayan ya gama, ya iya dawowa.

Post masu alaƙa

Atiku ya naɗa El-Rufai cikin mambobin kwamitin yaƙin zaɓensa

Yara mata 4 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa

Ba na jin haushin abokaina da suka yi shiru kan tsare ni — El-Rufai