Yanzu haka ana fargabar cewa mutane 11,587 sun kamu da cutar mashako yayin da aka tabbatar da mutane 7,202 a kananan hukumomi 105 daga jihohi 18 da ke fadin kasar sun kamu da cutar, inda cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 453 a Najeriya. Kashi 73 cikin dari na wadanda suka kamu da cutar yara ne yan shekara 1 zuwa 14.
Jihar Kano na daga cikin jihohin da cutar ta fi kamari, sauran jihohin sun hada da Yobe, da Katsina, da Barno, da Kaduna, da Jigawa, da Bauchi, da Legas, da Birni Tarayya Abuja, da Gwambe, da Osun, da Sakkwato, da Njeja, da Kuros Ribas, da Enugu, da Imo, da Nasarawa da kuma jihar Zamfara.
Daraktan tsare-tsare bincike da kidiggiga na hukumar lafiya matakin farko a Abuja Dr Abdullahi Bulama Garba yace hukumar su da sauran masu ruwa da tsaki abangaren lafiya sun dauki dukkan matakan dakile yaduwar ta inda tuni aka fara bada rigakafin cutar a wasu jihohi.