Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ce gwamnati ta ƙi amincewa da buƙatun masu garkuwa da mutanen da suka kai hari makarantu uku a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar a ranar 15 ga Mayu.
Maimakon haka, gwamnati ta mayar da hankali kan aikin ceto ɗaliban ne ta hanyar amfani da bayanan sirri, kamar yadda shafin jaridar Punch ya ruwaito a ranar 31 ga Yuli.
Tinubu ya bayyana haka ne a karon farko tun bayan da aka ceto aƙalla ɗalibai da malamai 39 a ranar 10 ga Yuli, yayin wata ganawa da tawagar sarakunan gargajiya daga jihar Oyo a Abuja.
Ya ce: “Mun ƙi tattaunawa kan biyan kuɗin fansa. Waɗannan masu aikata laifin sun buƙaci mu saki wasu daga cikin ‘yan ƙungiyoyinsu da aka riga aka kama. Wannan na daga cikin sharuɗɗansu, baya ga kuɗin da suke nema.”
Ya ƙara da cewa: “Mun ce babu wata yarjejeniya. Ba za mu tattauna da masu aikata laifi ba. Sun aikata kisan kai, kuma mun shirya murƙushe su. Suna da iyalai da kuma al’ummomin da suka fito.”
Har ila yau, Tinubu ya danganta ƙaruwar sace-sacen mutane da hare-haren masu tayar da ƙayar baya a Najeriya da matsalolin tsaro da ke ƙasashen yankin Sahel.