Masarautar Ukpo da ke ƙaramar hukumar Dunukofia ta bai wa shugaban ƙasa Bola Ahmad TInubu da mataimakinsa Kashim Shettima sarauta.
Masarautar dai ta ba wa shugaban ƙasar nan sarautar “Eze Udo of Igbo Land”, wato “sarkin zaman lafiya na ƙasar Igbo”, sai kuma mataimakinsa wanda aka ba shi sarautar, “Enyi Ndigbo”, wato “abokin al’ummar Igbo”.
A yayin wannan naɗin sarauta wanda mataimakin shugaban ƙasar nan, Kashim Shettima, ya wakilci shugaban ƙasa, ya ce suna sa ne da irin matsalolin da mutanen ƙabilar Igbo ke fama da shi kuma za su yi duk mai yuwuwa wajen ganin an magance musu matsalolinsu.
Sannan an rawaito cewa mataimakin shugaban ƙasar na cewa tuni yan ƙabilar ta Igbo suka fara samun jiga-jigai a sha’anin siyasar ƙasar nan.
Inda ya ba da misali da sanata Hope Uzodinma da sanata Dave Umahi da Hon. Ben Kalu da kuma na kwana-kwanan nan, wato sanata Ifeanyi Uba wanda ya dawo jam’iyyar APC waɗanda ya ce duk suna wakiltar ‘yan ƙabilar ta Igbo ne a siyasance.
A ƙarshe, Mataimakin shugaban ƙasar, ya yaba wa ‘yan ƙabilar da cewa su ne ruhin ƙasar nan, domin babu inda mutum zai shiga a ƙasar nan bai ga ‘yan ƙabilar Igbo ba, kuma in har babu su a waje, to wajen ka iya zama abin tsoro.