Yadda mutane suka je ɗiban ganima bayan faɗuwar tankar man fetur a Ibadan

wani sabon bidiyo ya sake nuna yadda wasu mutane ke ci gaba da jefa rayukansu cikin hadari yayin da suke kwasar man fetur daga tankar da ta yi hatsari.

RahotanniRahotanni daga birnin Ibadan sun ce wasu mazauna yankin sun taru a kan titin Academy zuwa Iwo Road, inda wata tankar mai ta kife, suka fara dibar man fetur duk da barazanar tashin gobara ko fashewa.

Bidiyon da aka wallafa a ranar Lahadi ya nuna jama’a na cika galan da kwantena da mai, ba tare da la’akari da hadarin da ke tattare da irin wannan aiki ba.

Hukumomi sun dade suna gargadi kan wannan dabi’a, wadda ke yawan janyo asarar rayuka a fadin Najeriya.

A cewar Hukumar  FRSC akalla mutane 411 ne suka mutu a shekarar 2024 sakamakon irin wadannan lamurra a fadin Nijeriya.

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai