Tsohon Kwamishinan ’yan sandan Najeriya a Jihar Kano CP Muhammad Wakili mai ritaya (Singham) ya ce samar wa matasa aiki zai iya magance balahirar ƙwacen waya.
Cp Wakili mai ritaya ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta TRT.
Tsohon Kwamishinan ya yi wannan jawabin ne a daidai lokacin da ake cigaba da asarar rayuka a sassan Arewacin Najeriya sakamakon ƙwacen waya.
A kasa da mako guda, rahotanni sun bayyana cewa masu ƙwacen waya sun halaka wani soja a kan gadar Kawo jihar Kaduna, sun kuma halaka wani a jihar Gombe.
- Hukumar Tace Fina-Finai Ta Yabawa Dakunan Taro tare da Gidajen Wasanni Bisa Bin Doka Da Oda A Kano
- An Kashe Mutane 7 A Filato
Ƙwacen waya da faɗan daba ya jima yana janyo asarar rayuka a jihar Kano da sassan Arewacin Najeriya.
Sai dai masana da dama baya ga CP Wakili mai ritaya sun sha bayyana rashin aikin yi tsakanin matasa a matsayin abin da ke kara jefa mutane cikin bala’in ƙwacen waya.