Rundunar ‘yan sandan Jihar Kogi ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun sace Hakimin Bagaji Odo, Alhaji David Wada, a yankin Ƙaramar Hukumar Omala.
Kakakin rundunar, SP Williams Ovye-Aya, ne ya bayyana haka a yayin da yake magana da manema labarai a garin Lokoja, ranar Talata, 2 ga watan Satumba, 2025.
A cewarsa, an samu kiran gaggawa daga ofishin ‘yan sanda na Omala inda aka sanar da sace basaraken yayin dawowarsa daga wani taro na majalisar sarakunan gargajiya da aka gudanar a Abejukolo, hedikwatar ƙaramar hukumar.
Rahoton ya nuna cewa ‘yan bindigar sun tare hakimin ne a kusa da kauyen Ojuwo Ugweche, inda suka yi awon gaba da shi zuwa cikin daji.
- Gwamnatin Tarayya Ta Bullo Da Sabuwar Manhajar Karatun Firamare Da Sakandire
- NDLEA Ta Kama Kwalaben Akuskura 8,000 Da Sinkin Tabar Wiwi 48 A Kano
Tuni jami’an tsaro suka kaddamar da samame tare da haɗin gwiwar mafarauta da ‘yan sa-kai domin bin sawun masu garkuwar da nufin ceto hakimin cikin aminci.
Shi ma babban basaraken Omala, Onu Ife Boniface Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da kira ga hukumomin tsaro da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kubutar da hakimin lafiya.
Har zuwa yanzu, ba a sami wata alaka da masu garkuwar ko wata bukatar fansa daga gare su ba.
Kamar yadda jaridar Arewa Updates ta wallafa.