NDLEA Ta Kama Kwalaben Akuskura 8,000 Da Sinkin Tabar Wiwi 48 A Kano

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Kano, ta kama kwalabe 8,000 na Akuskura da ake zargin na dauke da miyagun sinadarai, tare da sinkin  tabar wiwi 48.

A cikin sanarwar da Kakakin hukumar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari ya fitar a ranar Talata, 2 ga Satumba, 2025, ya bayyana cewa jami’an hukumar sun cafke wani mutum mai shekaru 37, mai suna Ali Muhammad, a kan titin Zariya zuwa Kano, kusa da gadar Tamburawa.

A cewar hukumar, jami’an NDLEA sun dakatar da wata babbar motar tirela mai dauke da kaya daga Legas zuwa Maiduguri, inda suka gano kayan a boye tsakanin baburan Adaidaita Sahu da tirelar ke dauke da su, Haka kuma, an yi amfani da katako wajen rufe wajen da aka boye kayan a kasa cikin tirelar.

Hukumar ta ce an mika kayan da wanda ake zargin ga jami’an bincike, kuma za a gudanar da karin bincike da gwaje-gwaje a dakin gwaje-gwaje domin tantance nau’in sinadaran da ke cikin kayan.

Kwamandan hukumar a Kano, ACGN A.I. Ahmad, ya gode wa Shugaban NDLEA na kasa, Birgediya Janar Buba Marwa (rtd), bisa goyon bayan da yake baiwa rundunonin gaba, wanda ke ba su damar gudanar da ayyukansu cikin nasara.

Hukumar ta kuma yi kira ga jama’a da su rika kai rahoton duk wani abu ko kaya da suke zargi, zuwa ofishin NDLEA mafi kusa ko kuma ga sauran hukumomin tsaro.

Post masu alaƙa

Hadejia ta cika shekaru 120 da cin nasara kan turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

NSCDC ta rufe wani gida da ake zargin ana safarar jarirai a Legos.

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta kama wanda ake zargi da safarar Alburusai a tankin Babur