Yan Daba Sun Wawushe Katinan Zabe PVC a Jihar Osun

Wasu da ake zargin yan daba ne sun kai hari ofishin hukumar zabe ta INEC a makarantar Oyinlola DC, Okuku da ke jihar Osun tare da sace katinan zabe.

Rahotanni sun ce maharan sun yi harbi a sama tare da tarwatsa jama’ar da ke wurin, kafin su kwashe katinan zabe na dindindin (PVC) dake cikin wasu kwalaye uku.

Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta fara bincike domin gano wadanda suka aikata laifin da kuma dawo da katunan da aka sace.

Post masu alaƙa

APC ta nada Abdulaziz Yari a matsayin jagoran kamfen na Tinubu

Zan mayar da tallafin man fetur idan na ci zaɓe – Atiku

Gwamnonin da ke shirin murɗe zaɓen 2027 za su sha mamaki — Kwankwaso