Yan Sanda Sun Kama Masu Safarar Bindigu Da Sauran Laifuka A Jigawa

Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta samu nasarar kama wasu mutane da ake zarginsu da safarar bindigu da miyagun kwayoyi tsakanin jahohin Plato da Kano da kuma Jigawa.

An kama wadanda ake zargin a karamar hukumar Kazaure dake jihar Jigawa lokacin da suke yunkurin shigo da bindigar jihar Kano.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Jigawa SP Shisu Lawan Adamu, ne ya bayyana  hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Lahadi.

Wanda ake zargin na farko, Abdussamad Haruna mai shekaru 30 mazaunin garin Dansure karamar hukumar Kazaure, an cafke shi dauke da bindigu kirar gida da kuma miyagun kwayoyi da aka yi safararsu daga jihar Plato.
sannan binciken yan sandan ya kai ga kama mutum na biyu mai suna Auwalu Yusuf dan shekaru 24 mazaunin Kofar Wambai Kano, inda aka kama shi da bindiga.

Sp Shisu Lawan ya kara da cewa sun kama barayin motoci, barayin Babura dilolin kwaya da kuma masu barnata dukiyar gwamnati da dai sauransu

kwamishinan yan sandan jihar , CP Dahiru Muhammad, ya rundunar ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yaki da masu aikata laifuka don samar wanzuwar zaman lafiya a fadin jihar.

Kayayyakin da aka kwato sun hada da robar Sholusho 239, tablets D5 guda 1000, Exol 1000, Tramadol 2,000 , kullin tabar Wiwi 129, babur 1 .

A karshe rundunar ta ce da Zarar ta kammala bincike zata gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda