An Kama Wanda Ake Zargi Da Kunnawa Tsohuwar Budurwarsa Wuta A Oyo

Rundunar yan sandan jihar Oyo, ta kama wani matashi mai suna Lawan Faruq, bisa zarginsa da kunnawa tsohuwar budurwarsa wuta, bayan ta yanke alakar soyayyar dake tsakaninsu.

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Wanda ake zargin ya cinnawa tsohuwar budurwar tasa wuta a barikin sojoji dake Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Rahotanni na cewa Lawal Faruq, ya dauki matakin kan zargin karya alkawari da masoyiyar tasa tayi na yanke alakar soyayyarsu, inda ya yi amfani da fetur ya zuba mata sannan ya kyasta ashana.

An garzaya da budurwar mai suna Omolola Hassan wani asibiti lokacin da jami’an sojoji suka kai mata daukin gaggawa.

 

 

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya