‘Yan Sandan Najeriya Sun Fara Aiwatar Dokar Inshorar Motoci

Daga: Safiyanu Haruna Kutama

Mai magana da yawun ‘yan sandan Najeriya a Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce wannan shirin na inganta insharar motoci zai tabbatar da cewa masu motoci masu bin tituna sun sami kariya.

‘yan sandan ya ce aiwatar da dokar, wanda aka fara a Legas a ranar Asabar, na bin umarnin Sufeto-Janar na ‘yansanda, Kayode Egbetokun, wanda ya bukaci a tabbatar da cewa duk masu ababen hawa sun mallaki inshorar motocin mai inganci.

Ya bukaci direbobi da masu ababen hawa su bi doka da oda, yana mai cewa wadanda suka saba za a hukunta su.

Mai magana da yawun ‘yan sanda ya kuma bukaci jami’an da ke aiwatar da dokar su nuna kwarewa a yayin gudanar da aikinsu.

Post masu alaƙa

Bwala yayi zargin akwai hannun kasashen wajen kan matsalar tsaro a Nijeriya

Dakarun yan sanda 200 sun samu horon sarrafa makami a Kano.

DSS ta kama waɗanda ake zargi da sace Farfesa A Nasarawa