’Yansanda sun kama mutane 193 tare da kwato makamai da kwayoyi a Kano

Rundunar ’yansandan Najeriya a jihar Kano ta kai samame wuraren da ake zargin maboyar masu aikata laifuka ne, inda ta kama mutane 193 tare da kwato makamai masu haɗari da kuma miyagun ƙwayoyi.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar a jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar.
A cewar sanarwar, daga cikin kayan da aka kwato akwai adduna, wuƙaƙe, goraye, da kuma miyagun ƙwayoyi irin su Pregabalin da tabar wiwi.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, ya bayyana cewa wannan samame na daga cikin matakan da rundunar ke ɗauka domin ƙarfafa tsaro da rage yawaitar laifuka a faɗin jihar, yana mai cewa bincike kan lamarin na ci gaba.
Rundunar ta kuma yaba wa jami’anta bisa ƙwazo da jajircewa, tare da gode wa al’umma kan haɗin kai da suke bayarwa. Haka zalika, ta buƙaci mazauna jihar da su riƙa kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga hukumomi domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai