Za mu baza jamai’anmu don samar wa Najeriya zaman lafiya

Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ce sojojin ƙasar za su yi duk mai yiwuwa don daƙile ƙaruwar hare-haren ƴanbindiga a jihar Neja da sauran sassan ƙasar.

A ƙarshen makon da ya gabata ne wasu mahara suka far wa Kasuwar Daji da ke jihar ta Neja, inda suka kashe fiye da mutum 40 tare da yin garkuwa da wasu kafin su ƙona kasuwar.

Laftanar Janar Shu’aib ya ce sojojin ƙasar za su mayar da hankali wajen aiwatar da umarnin shugaban ƙasa na kakkaɓe ayyukan ƴanbindigar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya ambato shi yana cewa.

Bayan harin na Neja shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaron ƙasar su yi duk mai yiwuwa don kuɓutar da mutanen da maharan suka sace a lokacin harin.

Post masu alaƙa

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP 

Kotun musulunci dake Jogana ta bayar da umarnin tsare mutanen da Ake tuhuma da yunkurin aikata tsafi.

Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin shekaru 490 ga tsohon shugaban bankin NEXIM.