Za mu kawo karshen cire wa mutane kudi da bankuna ke yi ~ CBN

Sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Olayemi Cardoso ya bayyana shirinsa na kawo karshen hauhawan farashin kaya da cire kuɗaɗe da bankin ke yi ga jama’a.

A yayin da Majalisar Dattawa ke tantance shi, Gwamnan bankin ya ce  “A kan maganar tashin farashin kayayyaki a kasar nan, wasu su na cewa rashin tsari ne yayin da wasu ke cewa yanayin samar da kuɗaɗe ne.

Ya ce “Maganar gaskiya ita ce matsalar ta shafi dukkan abubuwa guda biyun. Inda ya bayyana cewar, “Rahotanni sun tabbatar da cewa cikin shekaru 10 zuwa 15, kaso 50 na tashin farashin kaya ya samu ne daga matsalar yawaitar kudi a kasar nan.

Ya ƙara da cewar, “Wannan babbar matsala ce wacce dole a tinkare ta da karfi don kawo karshen wannan matsalar.”

Cardoso ya yi alkawarin cewa babban bankin zai yi duk mai yiyuwa don ganin matsalar rashin kudi bai zama matsala ba a kasar nan.

A jiya Talata 26 ga watan Satumba ne aka kammala tantance sabon gwamnan babban bankin ƙasar nan, Olayemi Cardoso bayan nadin da Tinubu ya masa a makon jiya.

A satin ne kuma Shugaba Tinubu ya nada mataimakan gwamnan bankin guda hudu na wa’adin shekaru biyar bayan tantance su a majalisa.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr