Zulum ya bai wa sojoji kyautar motocin yaƙi, ya tallafa wa ’yan gudun hijira

Farashin hannayen jari ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin Asiya, yayin da farashin mai ya ragu, bayan sanar da cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran.

Farashin ɗanyen man fetur na Brent ya fara sauka da kusan kashi huɗu cikin ɗari, inda ya ragu zuwa ƙasa da dala 84 kan kowace ganga.

Farashin man ya sakko ƙasa duk da rashin ƙarin bayani kan abun da ke ƙunshe cikin yarjejeniyar, abun da ke nuna yadda ‘yan kasuwa suka yi imanin cewa komi zai daidaita da zarar an sake buɗe mashigar Hormuz.

Kafin rikicin, kusan kashi 20 cikin ɗari na man fetur da iskar gas na duniya na bi ta wannan muhimmiyar hanya da ke yankin Tekun Fasha.

A lokacin da faɗan ya ɓarke, Iran ta kusan hana zirga-zirgar jiragen ruwa ta wannan mashiga gaba ɗaya.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Najeriya ta amince da biyan ma’aikata Naira 70,000 alawus din sufuri

An fitar da matar da ta kai cutar Ebola Najeriya daga ƙasar

Adadin mutanen da suka mutu a harin ƴanbindiga a Taraba ya kusa 50