Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zaɓi Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin abokin takararsa na mataimakin gwamna a Zaɓen 2027.
Mustapha Kwankwaso, wanda tsohon Kwamishinan Matasa da Wasanni ne a gwamnatin Abba Kabir Yusuf, ya yi murabus daga muƙaminsa, inda ya koma tafiyar mahaifinsa bayan rabuwar kai da ta shiga tsakaninsu da gwamnatin Jihar Kano.
Mai magana da yawun Ƙungiyar Kwankwasiyya, Habibu Saleh Mohammed ne ya tabbatar da hakan cikin wata taƙaitacciyar sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
“Mai girma Aminu Abdussalam Gwarzo ya ayyana Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin abokin takararsa na mataimakin gwamna a Zaɓen Gwamnan Kano na 2027,” in ji sanarwar.
Zaɓin Mustapha Kwankwaso na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar NDC ke ƙoƙarin ƙarfafa tasirinta a Kano, jihar da ake kallon tana da muhimmiyar rawa a siyasar ƙasar nan.
Ana sa ran dai nan gaba kaɗan jam’iyyar za ta fitar da ƙarin bayanai kan zaɓin da kuma shirye-shiryenta na tunkarar Zaɓen 2027.