• Home  
  • ‘Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi Duk Musulmai Ne
- Babban Labari - Labarai

‘Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi Duk Musulmai Ne

Hukumomi a jihar Kebbi sun musanta kalaman da wani ɗan majalisar Amurka ya yi cewa akwai yiwuwar ɗaliban da aka sace a jihar mabiya addinin Kirista ne. Shugaban ƙaramar hukumar Danko/Wasagu, inda lamarin ya faru, Hon Hussaini Bena, ya tabbatar da cewa dukkanin ƴan matan da aka sace, da mai gadin makarantar da aka harbe […]

Hukumomi a jihar Kebbi sun musanta kalaman da wani ɗan majalisar Amurka ya yi cewa akwai yiwuwar ɗaliban da aka sace a jihar mabiya addinin Kirista ne.

Shugaban ƙaramar hukumar Danko/Wasagu, inda lamarin ya faru, Hon Hussaini Bena, ya tabbatar da cewa dukkanin ƴan matan da aka sace, da mai gadin makarantar da aka harbe duk Musulmai ne.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, ɗan majalisar Amurkar Riley Moore ya buƙaci magoya bayansa su taya shi yi wa ƴan matan da aka sace da mutumin da aka kashe addu’a.

A cewarsa ” duk da ba mu da cikakken bayani game da lamarin, amma mun san an kai harin ne a wani yanki da ke da kiristoci da yawa a Arewacin Najeriya, wajibi ne gwamnati ta ƙara ƙoƙari wajen kawo ƙarshen wannan zaluncin”.

A ranar Litinin da asuba ne wasu ƴanbindiga riƙe da muggan makamai suka shiga wata makarantar kwana da ke garin Maga a jihar Kebbi, inda suka sace ɗalibai 25, amma biyu daga cikin suka samu nasarar kuɓuta.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai