Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta kama wani mai suna Ibrahim Mohammed, mai shekaru 21 mazaunin unguwar Rijiyar Zaki, da buhunan tabar wiwi huɗu da kuma sinƙi-sinƙi guda 297.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa da Muhasatvr.
Sanarwa ta ce an kama wanda ake zargin, bisa ci gaba da ake yi na tattara bayanan sirri, da aiki da fasahar zamani kamar yadda babban sufeton ƴan sandan Nijeriya, Kayode Adeolu Egbegtokun, ya bayar da umarni, don daƙile hada-hadar miyagun ƙwayoyi dake yin illa ga zamantakewar al’umma.
CSP Abdullahi Kiyawa, ya ƙara da cewa sun cafke wanda ake zargin a ci gaba da binciken wasu ƴan fashi da makami da suka kama.
Rundunar ta ce yanzu ta gudanar da bincike don kamo sauran waɗanda ake zargi da yin hada-hadar tabar wiwi da sauran kayan mayen da ake shigowa da su jihar Kano.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa jami’an da suka kama dilan miyagun ƙwayoyi, inda ya tabbatar da cewa da zarar an kammala bincike za a gurfanar da duk wanda yake da hannu akan lamarin.