Rundunar ‘yansanda a jihar Katsina ta kama wata mata mai shekaru 27, Hadiza Ibrahim, bisa zargin satar kayayyaki daga wani shago da darajarsu ta kai naira miliyan 10.1.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Aliyu Abubakar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya ce an kama matar ne bayan samun rahoto daga jami’in tsaron shagon Green House da ke Katsina a ranar 4 ga watan Maris.
A cewarsa, an bayyana matar a matsayin gogaggiyar ‘yar satar shago da ke gudanar da ayyukanta a cikin birnin.
Abubakar ya ce kayayyakin da aka sace sun kai kimanin naira 10,102,000, yana mai cewa an gano laifin ne ta hanyar hotunan CCTV na shagon, inda aka hango matar tana satar kayayyaki daban-daban.
“Bayan nazarin bidiyon CCTV, an bi sahunta har zuwa inda aka kama ta,” in ji shi.
Ya kara da cewa bayan gudanar da bincike a gidanta, an gano kayayyaki masu darajar wannan kudi.
Kayayyakin da aka kwato sun hada da takalma guda 274, mayafi guda 37, kayan wasanni guda 67, kayan yara guda 54, hula guda 123, safa guda 315, zanen mata guda 45, jakunkuna guda 9, kwalayen taliya guda 3, turare guda 24, da kwalayen sabulu guda 5.