10% Na ‘Yan Firamare Din Kano Ne Iya Karatu Da Kyau-UNICEF

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce Kashi 9.6 cikin 100 na daliban makarantun firamare a jihar Kano ne kawai ke nuna kwarewar karatu, kuma kashi 11.2 cikin 100 ne ke da ilimin lissafi.

Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Mohammed farah, ce ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano a ranar bikin ilimi ta duniya ta 2025.

Mohammed ya bayyana kididdiga na malejin lissafi na shekarar 2021 (MICS), Mohammed ta ce yara 989,234 da suka isa shiga makarantar firamare a Kano—kimanin kashi 32 cikin 100 na daliban.

Domin magance matsalan, Muhammed ya ce UNICEF ta kaddamar da ayyuka, ciki har da shigar da makarantun kur’ani a tsarin ilimin Boko. Ya ce sama da malaman kur’ani 290 da masu kula da makarantun kur’ani na jihohin Kano da Jigawa ne aka horas da su a karkashin wannan shiri domin ganin yara sun samu ilimin boko tare da karatun addini.

“UNICEF ta kuma tallafa wajen gine-gine tare da gyara magudanar ruwa, tsaftar muhalli na (WASH) a makarantu 33 da ke fadin Kano da Jigawa. Wadannan yunƙurin sun amfana kai tsaye yara 39,432—maza 19,810 da mata 19,622—ta hanyar inganta kayan aikin makaranta da riƙon ɗalibai,”

UNICEF ta bayyana kokarin inganta ilimi ta hanyar horas da malamai 1,109 a fannonin karatu, da bunkasa yara kanana, “Bugu da kari, mun samar da kayayyakin koyarwa sama da 630,249 ga makarantu, wadanda ke taimaka wa kananan yara a wajen karantar da su a makarantun firamare. “in ji Malam RAHAMA RIHOOD MOHAMMED FARAH, Shugaban ofishin UNICEF na shiyar kano, jigawa, katsina.

Post masu alaƙa

Ba za mu buɗe Hormuz ba sai Amurka ta buɗe tashar ruwanmu – Iran

Jirgin ‘yan cirani ya kife a tekun Libiya

Da buƙatar samar da takin zamani ga manoman Najeriya – MDD