Masu Unguwanni 13 Sun Yi Murabus Daga Mukamansu A Jihar Kano.

Hakimin gundumar Jogana da ke ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano, Abdulkadir Muhammad Balarabe, ya amince da murabus ɗin wasu masu unguwanni su goma sha uku a ƙasarsa, waɗanda suka yi murabus don ƙashin kansu.
‎
‎Abdulkadir Muhammad Balarabe, ya bayyana hakan ne a yayi zantawar sa da manema labarai ranar Talata 02 ga watan Satumban 2025, a gundumarsa ta Jogana da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar Kano.
‎
‎Abdulkadir Muhammad, ya kuma ce masu unguwannin da suka sauka da kansu, dukkaninsu sun rattaɓa hannu a takarda.

“A cikin takardar sun bayyana cewa sun sauka saboda an kawo ƙarar wani Mai unguwa da yake zaluntar al’ummarsa suka ce indai akayi masa hukunci za su sauka da kuma hakimin ya hukuntashi suka ce sun sauka daga kan mukamansu, in ji shi”.

 

Post masu alaƙa

Dangote, Habasha da Djibouti za su gina bututun mai na dala miliyan 600

Atiku ya naɗa El-Rufai cikin mambobin kwamitin yaƙin zaɓensa

Sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa na haifar da sakamako mai kyau – Shettima