7
Gwamnatin Jihar Kaduna, tare da haɗin guiwar Hukumar Ci gaban Afirka ta Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AUDA–NEPAD) reshen Najeriya, sun kaddamar da rabon kayan noma ga kananan manoma 400 a fadin jihar.
Da yake jawabi a yayin taron bada tallafin, wanda aka gudanar a gidan tarihi na Arewa House da ke jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani, ya baiyana tallafin a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba a ƙoƙarin gwamnatin jihar wajen sauya fasalin harkar noma da kuma ƙarfafa yawan amfanin gonar, la’akari da yadda Noman ya kasance ginshiƙin tattalin arzikin jihar.
Gwamnan wanda Kwamishinan Noma, Murtala Dabo, ya wakilta ya kara da cewa wannan haɗin guiwa na nuni da yadda gwamnatin ke mai da hankali kan ci gaban da ya shafi jama’a kai tsaye, tare da daidaita gina tattalin arziki da kuma samar da wadataccen abinci, harma da dorewar haɗin kai, adan haka aka ware wa bangaren noma fiye da naira Bilyan 10 a kasafin kudin shekarar 2025.

A cewar sa, “Manoma ƙanana su ne ginshiƙin tsarin noman mu adan haka muka tallafa musu da nufin ƙarfafa tattalin arziki, tabbatar da wadatar abinci, da kuma inganta rayuwar dubban Iyali, wanda kuma a halin yanzu Jiharmu ce jihar da ta cika ka’idojin da aka shimfiɗa a yarjejeniyar Malabo kan saka hannun jari a harkar noma”.
A nasa bangaren shugaban Hukumar Ci gaban Afirka ta Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AUDA–NEPAD) na Najeriya, Hon. Jabir Abdullahi Tsauni, ya yabawa Gwamnatin Kaduna bisa samar da kudaden haɗin guiwar da suka bada damar faɗaɗa shirin zuwa dukkan kananan hukumomin jihar 23.