Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC, ya zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da taimaka wa Shugaba Bola Tinubu, a fakaice domin ya lashe zaɓen 2027.
Wannan na zuwa ne bayan da Kwankwaso ya nemi Atiku Abubakar, ya janye wa Peter Obi takararsa.
Atiku Abubakar ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, yayin da Kwankwaso yake mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, mai magana da yawun kwamitin ADC, Kola Ologbondiyan, ya bayyana kiran Kwankwaso a matsayin son kai da kuma yunƙurin raunana ’yan adawa.
Ologbondiyan ya ce maimakon Kwankwaso ya mayar da hankali wajen ƙalubalantar gwamnatin Tinubu, ya fi karkata ga sukar ɗan takarar ’yan adawa.
Ya kuma jaddada cewa Atiku zai lashe zaɓen shugaban ƙasa a Jihar Kano a 2027 ko babu goyon bayan Kwankwaso.
Ya zargi Kwankwaso da fifita burinsa na siyasa a kan muradun ’yan adawa, yana mai cewa matakansa na iya amfanar da jam’iyyar APC mai mulki.
Sai dai, waɗannan zarge-zarge ra’ayin kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC ne.