Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi watsi da jita-jitar cewa jam’iyyarsa na yi wa jam’iyyar APC mai mulki aiki domin ta lashe zaɓen 2027.
Hakazalika, ya musanta zargin cewa NDC za ta janye daga zaɓen shugaban ƙasa na 2027 domin mara wa jam’iyyar ADC baya.
Kwankwaso ya ce tikitin takarar shugaban ƙasa na NDC, wanda Peter Obi ke jagoranta, yana nan daram kuma suna da yaƙinin lashe zaɓen.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon gwamnan Jihar Kano, ya zargi kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC da mayar da hankali wajen sukarsa, da Peter Obi da kuma jam’iyyar NDC, maimakon tallata ɗan takararsu ga ’yan Najeriya.
Ya bayyana iƙirarin cewa NDC tana yi wa jam’iyyar APC mai mulki aiki ko kuma tana shirin janyewa domin goyon bayan ADC a matsayin ƙarya da nufin yaudarar masu zaɓe.
“Ba za mu janye takararmu domin ADC ko wata jam’iyya ba. Muna da yaƙinin cewa muna da ƙwarewa, cancanta da shirin da ake buƙata domin jagorantar Najeriya,” in ji shi.
Kwankwaso ya zargi kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC da yaɗa bayanan da ba su da tushe game da jam’iyyarsa.
Ya kuma gargaɗi magoya bayan NDC da su yi watsi da duk wani rahoto da zai nuna cewa jam’iyyar ta amince da wani ɗan takara ko ta janye daga zaɓen shugaban ƙasa.
Ya shawarci kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC da ya mayar da hankali wajen amsa zarge-zargen da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi wa ɗan takararsu, maimakon sukar shugabannin NDC.
Kwankwaso ya jaddada cewa tikitin takarar NDC ba ya yi wa APC ko wani daga cikin ’yan takararta aiki.
“Tikitin OK ba ya yi wa APC ko wani daga cikin ’yan takararta aiki, kuma ba ya wakiltarsu. Ba mu ga wata dama ko dalilin da zai sa mu janye daga zaɓen shugaban ƙasa domin goyon bayan ɗan takarar ADC ko wani daban ba,” in ji shi.
Ya kuma soki gwamnatin APC, yana zarginta da gazawa wajen biyan buƙatun ’yan Najeriya.
Sai dai ya ce ADC ma ba ta da wata mafita ta daban ga ƙasar.
Kwankwaso ya bayyana NDC a matsayin jam’iyyar adawa mafi ƙarfi a Najeriya, tare da kira ga magoya bayanta da su ci gaba da jajircewa domin ganin jam’iyyar ta lashe zaɓen 2027.
Ya ce jam’iyyar za ta mayar da hankali wajen magance matsalar tsaro, inganta ilimi da noma, bunƙasa ababen more rayuwa da kiwon lafiya, farfaɗo da tattalin arziƙi, da kuma ƙarfafa haɗin kan ƙasa.
“Najeriya za ta gyaru,” in ji shi.