• Home  
  • An Samu Hatsaniya Tsakanin Matasa Da Jami’an Tsaro A Kano
- Babban Labari - Labarai

An Samu Hatsaniya Tsakanin Matasa Da Jami’an Tsaro A Kano

An samu hatsaniya a tsakanin wasu matasa da jami’an tsaro a kan sabon titin Mandawari dake birnin Kano.

A yayin da aka shiga wuni na uku da fara zanga-zangar tsadar rayuwa a fadin ƙasa, an samu hatsaniya a tsakanin wasu matasa da jami’an tsaro a kan sabon titin Mandawari dake birnin Kano.

Tuni dai zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali inda ta haifar da sanya dokar hana fita da har yanzu ake zaune cikin yanayi na zullumi.

A cewar shaidun gani da ido, matasan sun fito titin ne domin shaƙatawa, inda su kuma jami’an ‘yan sandan yankin da sojojin da ke sintiri suka buƙaci su koma gida, amma hakan ba ta samu ba. 

Wannan turjiya da matasan suka yi wa jami’an tsaron ne ya sa ka harba borkonon tsohuwa domin tarwatsa su.

Abokin aikinmu Hassan Abdu Mai Bulawus ya yi iya kokarinsa domin jin ta bakin mai Magana da Yawun ‘Yan Sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, amma haƙarmu ba ta cim ma ruwa ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai