- Babban Labari - Labarai

An Sace Amarya A Sakkwato

’Yan Bindiga dauke da muggan makamai sun sace wata amarya da ƙwayenta huɗu a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato

Wasu ’Yan Bindiga dauke da muggan makamai sun sace wata amarya da ƙwayenta huɗu a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato ranar Asabar. 

‘Yan bindigar sun sace amaryar da kawayenta ne a garin Kwaren Gamba, da ke yankin Kuka Teke.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan kauye na fama da hare-hare daga yaran kasurgumin dan ta’addan nan Bello Turji.

Wadan da suka shaida faruwar lamarin  sun ce ‘yan bindigar sun afka wa yankin sannan kuma tafi da waɗanda abin ya shafa, lamarin da ya jefa tsoro da tashin hankali a zukatan mazauna yankin.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000