• Home  
  • An Sace Wani Matashi A Kano
- Babban Labari - Labarai

An Sace Wani Matashi A Kano

Wasu ‘yan ta’adda masu satar mutane sun yi garkuwa da wani matashi mai shekaru 20, Muhammed Bello a ƙauyen Zakirai da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa ta Jihar Kano.

Wasu ‘yan ta’adda masu satar mutane sun yi garkuwa da wani matashi mai shekaru 20, Muhammed Bello a ƙauyen Zakirai da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa ta Jihar Kano.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne yayin da ’yan bindigar suka kai hari a gidan Alhaji Yusha’u Ma’aruf, wanda yake da wani asibiti mai zaman kansa a ƙauyen na Zakirai.

Kazalika, wani ɗan gidan mai suna Abubakar Yusha’u mai shekaru 23 ya samu rauni yayin da ’yan bindigar suka guntule masa yatsa ɗaya a hannunsa na hagu.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:15 na dare, inda maharan su uku riƙe da bindigogi da adduna suka rufar wa gidan Alhaji Yusha’u.

Kazalika, maharan sun arce da wayoyin hannu da kuɗaɗe da ba a kai ga tantance ko nawa ba ne.

Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin da bincike ya soma gudana a kansa.

SP Kiyawa ya ce tuni ’yan sanda suka fara farautar ɓata-garin domin ceto matashin da aka yi garkuwa da shi.

An ruwaito cewa, a bayan nan ne ’yan sanda suka kama wasu mutum huɗu da ake zargin ’yan bindiga ne, sannan ta ƙwace makamai da alburusai da kuɗi kimanin naira 1,028,800 a unguwar Hotoro da ke Jihar Kanon.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai