Alkaluman waɗanda ambaliyar ruwa ta kashe a jihar Neja ya kai mutum 110, a cewar hukumar ba da agajin gaggawa na jihar.
Masu aikin ceto sun ce sun gano gawawwaki da dama.
Jami’ai a yankin Mokwa wurin da lamarin ya faru, sun yi gargaɗin cewa ƙarin mutane na cikin barazana a birnin.
An shafe tsawon sa’o’i ana tafka mamakon ruwan sama a yankin ranar Laraba, inda ruwa ya tafi da gidaje aƙalla 50.
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliya a kusan rabin jihohin ƙasar 36.
Sama da mutum 1,200 ne suka mutu sakamakon ambaliya a bara sannan sama da miliyan ɗaya suka ɗaiɗaita, a ambaliyar da ba a taɓa gani ba cikin gomman shekaru.

