Rundunar yan sandan jihar Kano, ta gurfanar da mutane 29 a gaban kotun majistiri mai 20 dake zaman ta, a rukunin Kotunan Noman Sland bisa zargin su da aikata laifukan dabam-daban ciki harda zargin kashe Bature yan sandan ƙaramar hukumar Rano CSP Baba Ali.
Lauyar gwamnatin jihar Kano, Barista Saima Garba, ta roki kotun ta bayar da damar a karanto musu kunshi tuhumar da ake yi musu yi ,inda kotun ta ba wa jami’inta umarnin karanto musu kunshi tuhume-tuhumen.
Ana zargin su da hada kai dayin barna ta hanyar kunna wuta, shiga ta laifi bada izini ba da yin sata da kuma kisan kai, wanda hakan ya sabawa sashe na 97, 114, 337, 350, 247,287,390 da kuma sashi na 221 na kundin penel code.
Kotun ta tambayi waɗanda ake tuhumar ko sun fahimci abinda aka karanta musu nan take suka amsa da cewa sun gane abinda aka karanta musu.
- Kisan DPO Rano: Yan Sanda Sun Gano Bindiga AK-47 Ta Bogi A Gidan Wanda Ake Zargi
- Mutane 7 Sun Rasu A Hatsarin Kwale-kwale A Sokoto
Wasu daga cikin wadanda ake tuhumar sun hada da, Yusuf Baba, Bala Mohd, Abdurrashid Ibrahim, Abdullahi Salisu Kere, Dadi Buhari, Inusa Adamu, Musa Munkaila, Mamuda Muhammad da Usman Shu’aibu.
Sauran sune Musa Hassan (Black) Abdurrashid Munkaila, Umar Ado Nadada ,Sabi’u Abubakar Sabi’u da kuma wata mace mai suna Ladi Ismail da ake zargin ta da tunzura matasan da suka kone gidajen wasu mutane a garin Rano.
Wakilan mu Mujahid Wada ya ruwaito mana cewa Alkaliyar kotun mai shari’a, Fauziyya Isah She she, ta dage ci gaba da sauran shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Yuni 2025 don sake gabatar da su a gaban kotu, inda ta yi umarnin a tsare su a gidan yari.
Haka zalika akwai sauran mutane kusan 20 da ake nema ruwa a jallo

