ACF Ta Yi Allah-Wadai Da Rushe Kasuwar Alaba Rago

Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya (ACF) ta bayyana matuƙar damuwarta kan rushe kasuwar Alaba Rago mai ɗimbin tarihi a Legas, inda ta bayyana hakan a matsayin babban koma baya ga dubban ’yan kasuwa.

A cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Farfesa T. A. Muhammad-Baba, Ƙungiyar ta bayyana cewa duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba, ɓarnata kasuwanci da dukiyoyi ya jefa wasu iyalai da dama cikin ƙunci.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Rushe kasuwar mai ɗimbin tarihi ya haifar da asarar kasuwanci da dukiyoyi, tare da kawo cikas ga hanyoyin rayuwar jama’a da haifar da matsaloli ga dubban mutane, ba a bayyana asarar rai ba.

Kungiyar ta ACF ta jajanta wa waɗanda rusau ɗin ya rutsa da su, inda ta buƙace su dage wajen yin haƙurin lamarin.

“Da fatan, waɗanda lamarin ya shafa za su kasance masu juriya masu ƙwazo, za su zo su taka rawa wajen taimaka wa waɗanda abin ya shafa su jure asarar da aka yi musu sanadin rushewar,” in ji Farfesa Muhammad-Baba.

Kungiyar ta bayyana cewa tana neman ƙarin bayani kan lamarin don jawo hankalin gwamnatin Jihar Legas da kuma al’ummar da abin ya shafa don magance matsalar.

A halin da ake ciki, ACF ta buƙaci gwamnati ta sa baki cikin gaggawa don taimaka wa waɗanda abin ya shafa.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda