SURE4U Ta Nada Dr. Gwani Farouk Umar A Matsayin Jakadanta

Gidauniyar Sure4U mai taimaka wa marasa ƙarfi da zawarawa da marayu ta gudanar da taron naɗa Dr Gwani Farouk Umar a matsayin Jakadanta na biyar.
An gudanar da taron ne a ɗakin taro na gidauniyar da ke MUHASA HOUSE, a Unguwar Farm Centre dake brinin Kano.

Da yake ƙarin haske a kan naɗin, Daraktan Tsare-tsare na gidauniyar ta Sure4U, Mannir Yari, wanda ya yi bayani a Madadin Mamallakin gidauniyar, Alhaji Muhammad Babandede, OFR, OCM, ya ce sai da suka yi nazari suka naɗa Dr. Gwani Faruk, a matsayin Jakadan na su, duba da gudunmawar da zai iya bai wa tafiyarsu.

A nasa bangaren Shugaban Kwamitin Amintattu na gidauniyar, Sanata UK Umar ya ce yana da kyakkwawan fatan naɗin na Dr. Gwani Faruk, domin kwalliya zata biya kudin sabulu.

Shi ma Abubakar Idris Ahmad Babban Jami’I a Hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano ya taya gidauniyar Sure4U murnar rabauta da Gwani Dr. Umar Faruk.

A nasa martanin dangane da naɗin, Ambassada Dr Gwani Faruk Umar ya gode wa gidauniyar ta Sure4u da ta zaɓe shi, tare da shan alwashin bai wa mara ɗa kunya.

Daga ɓangaren masana tsaro, Janar Idris Bello Dambazau, mai rataya, ya ce aikace-aikacen gidauniyar ta Sure4u abin alfahari ne ga yankin Arewacin Nijeriya.

 

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda