Babu Kawancen Da NNPP Ta Kulla Da Wata Jam’iyyar — Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya Sanata Rabi’u Kwankwanso ya ce suna jin daɗin jam’iyyarsu, kuma a halin da ake ciki babu wani ƙawance da suka ƙulla da wata jam’iyya.

Yayin da yake jawabi a wajen taron majalisar ƙoli na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja, Sanata Kwankwaso ya ce ba gaggawa suke yi ba.

”Ƴaƴan jam’iyyarmu ba gaggawa suke yi ba, komai muna yinsa a hankali”, in ji shi.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce ya ce kawo yanzu babu wata jam’iyya da suke tattaunawa da ita domin ƙulla ƙawance, sai dai ya ce hakan ba yana nufin ba za su tattauna da wata ba.

”Mu ƴansiyasa ne kuma a shirye muke mu tattauna da duk wanda ke son tattaunawa da mu”, in ji.

An dai jima ana raɗe-raɗin Kwankwaso zai koma jam’iyyar APC, tun bayan zaɓen 2023, inda har aka riƙa hasashen ba shi minista, lokacin da Tinubu ya ce zai yi aiki da ƴan hamayya a gwamnatinsa.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya