Ambaliya ta mamaye wasu sassan Abuja

Mamakon ruwan sama da aka yi a Abuja ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassan Babban Birnin Tarayya, Abuja lamarin da ya jefa mazauna yankunan cikin halin ƙunci tare da katse zirga-zirga.

Daga cikin wuraren da ambaliyar ta fi shafa akwai Wuse 2, musamman titin Adetokunbo Ademola, inda ruwa ya mamaye hanyoyi da muhallai.

Bidiyoyi da suka karaɗe kafafen sada zumunta sun nuna yadda motoci da dama suka nutse a cikin ruwa ko kuma suke yawo sakamakon kwararowar ambaliyar.

Haka kuma an ga direbobi da fasinjoji sun makale a wasu hanyoyi yayin da ruwa ya hana ababen hawa wucewa.

Ambaliyar ta kuma shafi yankunan Gudu, Lokogoma da hanyar da ke haɗa Gaduwa da Durumi, inda ruwa ya mamaye gada tare da hana zirga-zirga.

Wasu ‘yan kasuwa sun rufe shaguna bayan ruwa ya shiga wuraren kasuwancinsu, yayin da mazauna yankunan suka yi kira ga hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa.

Lamarin ya sake tayar da hankali kan matsalar magudanan ruwa a Abuja, musamman ma bayan hukumomin hasashen yanayi sun yi gargadin yiwuwar aukuwar ambaliya a birnin a bana.

Post masu alaƙa

Najeriya za ta fara ƙera motocin yaƙi da na’urorin daƙile daƙike ‘drone’

Sojojin sun kashe ‘ƴan ta’adda’ tare da ƙwace abubuwan fashewa 180 a Zamfara

INEC ta kai wa CBN ajiyar muhimman kayan zaɓen Gwamnan Osun