Gwamnonin da ke shirin murɗe zaɓen 2027 za su sha mamaki — Kwankwaso

Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewar gwamnonin da suke ganin za su iya amfani da ikon gwamnati wajen yin maguɗi a zaɓen 2027, za su sha mamaki.

Tsohon gwamnan na Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Abuja ranar Lahadi.

Ya ce wasu gwamnonin da suka kasa biyan buƙatun al’ummarsu suna komawa jam’iyyar APC mai mulki, saboda suna ganin jam’iyyar za ta taimaka musu su sake lashe zaɓe.

Kwankwaso ya ce ƙara da cewar taɓarɓarewar matsalar tsaro, talauci, rashin aikin yi da kuma rashin aiki na iya yin tasiri kan yadda ’yan Najeriya za su yi zaɓe a 2027.

Ya ce ’yan Najeriya suna ƙara fahimtar siyasa kuma za su iya ƙin zaɓar gwamnonin da sauran ’yan siyasa da ke neman wa’adi na biyu, ko da kuwa suna da ƙarfin gwamnati.

Ya ce: “Abin da nake hasashe shi ne, yawancin gwamnonin da za su nemi sake tsayawa takara a 2027 za su sha mamaki saboda jama’a ba za su goyi bayansu ba.”

Kwankwaso ya ce ’yan Najeriya suna da cikakken haƙƙin neman ingantaccen shugabanci, musamman ganin yadda yara da yawa ke fama da rashin zuwa makaranta da kuma yadda rashin tsaro ke ci gaba da shafar al’ummomi a faɗin ƙasar.

Ya bayyana cewar lokacin da yake gwamnan Kano, gwamnatinsa ta mayar da hankali kan ilimi ta hanyar inganta ilimin firamare, sakandare da manyan makarantu.

Ya kuma ce gwamnatinsa ta ƙaddamar da shirye-shiryen magance matsalar Almajirai tare da gina cibiyoyin ilimi, ciki har da samar wa ɗalibai wuraren kwana.

A cewarsa, abin da ya faru a Kano ya nuna cewa gwamnati za ta iya inganta rayuwar jama’a idan aka yi amfani da kuɗaɗen gwamnati yadda ya kamata.

Kwankwaso ya kuma soki ’yan siyasar da ke barin jam’iyyun adawa zuwa APC, yana cewa wasu daga cikinsu suna yin hakan ne don su yi nasara a zaɓen 2027.

Sai dai ya ce yana da yaƙinin cewa a ƙarshe, masu zaɓe ne za su yanke hukuncin wanda zai yi nasara a zaɓen.

Post masu alaƙa

Zan tabbatar matatun man Najeriya sun koma aiki – Tinubu

Majalisar dokokin Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi uku

Uba Sani ya ɗauki Jerry Adams mataimakinsa a Zaɓen 2027