Shahararriyar jarumar Kannywood ta samu ƙaruwa da mai gidanta
Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Rahama MK, wadda aka fi sani da Hajiya Rabi Bawa Mai Kada ta cikin shirin fim mai dogon zango na kwana casa’in ta haifi santaleliyar jaririya a gidan mijinta na gaske.