Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Yi Taro Kan Tsaro Da Tattalin Arziƙi A Taraba
Gwamnonin Jihohin Arewa maso Gabas, sun koka kan matsalolin da suka shafi ayyukan jin-ƙai da kuma gina muhimman ababen more rayuwa duk da ci gaban da aka samu a yaƙi da ta’addanci a yankin. Wannan bayani ya fito ne daga sanarwar ƙarshen taronsu karo na 12 da aka gudanar a Jalingo babban birnin Jihar Taraba. […]