Kwastam Ta Kama Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 48.5 A Kaduna

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta bayyana cewa jami’anta sun kama tabar wiwi mai darajar naira miliyan 48.5 da wasu kayan da aka haramta na naira miliyan 220 a Jihar Kaduna kamar yadda Gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Kwamandan hukumar ya ce an kama kayayyakin ne a ayyuka daban-daban da aka gudanar ranar 21 ga Agusta, 2025.

Ya ce jami’an sashen bisa ingattatun bayanan da suka samu ne suka tsayar da mota a Zaria kan babbar hanyar zuwa Kano inda suka yi nasarar kama tabar wiwi ɗin da sauran kayan da aka haramta.

Mai magana da yawun hukumar kwastam ya ce an miƙa wanda ake zargin da kayan ga jami’an hukumar yaki da ƙwayoyi ta Nigeria (NDLEA) don ci gaba da bincike da gurfanarwa a gaban shari’a bisa tsarin haɗin gwiwar hukumomi.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda