An Dage Shari’ar Nnamdi Kanu Saboda Rashin Shiri

Ba a ci gaba da shari’ar jagorar ƴan tawayen Bifra, Nnamdi Kanu ba kamar yadda aka shirya yi a ranar Juma’a.

Kanu wanda ke kare kansa ya shaida wa babbar kotun tarayyar da ke zamanta a Abuja, babban birnin Najeriya cewa, bai samu takardun ƙarar ba, don haka yana ɓuƙatar lokaci.

Wanda ake tuhumar ya kuma buƙaci kotun da ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, sun dinga bari ana ganinsa a kullum, saɓanin ranaku uku, litinin, laraba da juma’a da ake ganinsa a yanzu.

“Mai shari’a ina da masu bayar da shaida 23 da zasu zo daga ƙasashen duniya domin shari’ar, don haka ina buƙatar lokaci,” In ji Kanu.

An ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar Litinin mai zuwa.

A ranar Alhamis ne Nnamdi Kanu ya sallami duka lauyoyin da ke kare shi, inda ya sanar da kotun cewa zai ci gaba da kare kansa.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda