Shu’aibu Abdulkadir Da Ake Tuhuma Da Halaka, Rumaisa Ya Musanta Zargin A Gaban Kotu.

Babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Farida Rabi’u Danbaffa, ta ci gaba da sauraron shari’ar tuhumar da ake yi wa, Shu’aibu Abdulkadir da zargin kisan kan wata matar aure mai suna Rumaisa Shu’aibu.

A zaman kotun na yau Alhamis, lauyan gwamnatin jihar Kano, Barista Basiru Kabiru Aliyu, ya roki kotun karkashin sashi na 273 ACJL 2019 don a karanto kunshin tuhumar da ake yiwa wanda ake zargin, inda kotun ta amince.

Wani jami’in kotun ya karanta wa Sha’aibu Abdulkadir Chediyar Kuda , kunshin tuhumar kisan kan matar aure Rumaisa Shai’aibu, a ranar 6 ga watan Afrulun 2025.

Sai dai wanda ake zargin ya musanta kunshin tuhumar da ake yi masa.

Lauyan gwamnatin jihar Kano, Barista Basiru Kabiru Aliyu, ya roki kotun ta basu wata rana don kawo shaidun su da za su tabbatar da ya aikata laifin.

Sai dai lauyan dake kare wanda ake tuhuma Barista Mustapha Idris ,ya roki kotun da a basu kwafin kundin binciken shari’ar.

Wakilin mu Mujahid Wada ya ruwaito mana cewa mai shari’a, Farida Rabi’u Danbaffa, ta dage ci gaban sauraren shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Nuwamban 2025 tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsere wanda ake zargin.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda