Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Abubakar Sa’ad III ya bayyana cewa an ga watan Shawwal a Najeriya dan haka za a idin ƙamar salla ranar Lahadi.
Tun da yammacin ranar Asabar ne dai aka bayyana ganin watan Shawwal a ƙasar Saudiyya, kafin daga bisani a samu labarin ganin shi a jamhuriyar Nijar.
- An Ga Jinjirin Watan Shawwal A Saudiyya.
- Yan Sanda Sun Munsanta Labarin Kone Yan Kabilar Igbo A Kano.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana ganin watan ne a fadar sa da ke Sakkwato, Arewa maso yammacin tarayyar Najeriya kamar yadda ya saba.
Kawo yanzu dai ‘yan Najeriya na cigaba da bayyana murnar kammala ibadar watan Ramadan, suna kuma fatan Allah ya karɓa.