Home » An kafa kwamiti Kan Sabon Mafi ƙarancin Albashi A Kano

An kafa kwamiti Kan Sabon Mafi ƙarancin Albashi A Kano

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Gwamnatin Kano ta dauki tsattsauran mataki kan asibitoci uku saboda sakacin aiki

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta kafa kwamitin da zai dubi yiwuwar ƙaddamar da sabon mafi ƙarancin albashi sa’o’i 48 bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattabawa ƙudurin hannu. 

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ne na farko a gwamnonin Najeriya da ya kafa irin wannan kwamiti.

A ranar Talata ne dai mataimakin gwamnan, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya bayyana kwamitin a fadar gwamnatin jihar, ta hannun mai magana da yawunsa brahim Garba Shuaibu.

Ya ce, kwamitin zai tsara yadda za a aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi da kuma bayar da shawarwari ga gwamnatin jihar.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce, aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin zai ƙara bunƙasa ci gaba a Jihar.

Gwamnan ya ba kwamitin makonni uku ya gabatar da rahotonsa. Ya kuma bayyana cewa an zaɓi mambobin ne bisa cancanta, kuma ana kyautata musu zato.

Sanarwar ta bayyana Alhaji Usman Bala Muhammad a matsayin shugaban kwamitin, wanda a yanzu shi ne mashawarci na musamman ga gwamnan kan harkokin jihar.

Alhaji Usman Bala Muhammad ya yi godiya ga amanar da gwamnatin ta damƙa musu, inda ya ce aikin kwamitin zai yi tasiri sosai ga ma’aikata a jihar.

Sanarwar ta kuma bayyana Kwamishinan kuɗi na jihar Ibrahim Jibril Fagge da Musa Suleman Shanono Kwamishinan kasafi da tsare-tsare, da Baba Halilu Dantiye Kwamishinan yaɗa labarai, da Baffa Sani Gaya a matsayin mambobin kwamitin.

Hakazalika daga cikin mambobin kwamitin an bayyana Farfesa Aliyu Isa Aliyu da Salahudeen Habib Isa da Ibrahim I. Boyi da Ibrahim Muhammad Kabara da Mustapha Nuraddeen Muhammad da Abdulkadir Abdussalam da Umar Muhammad Jalo sai Hassan Salisu Kofar Mata da kuma Yahaya Umar a matsayin mambobin kwamitin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi a jihar Kano.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?