Ƴan ƙungiyar Jama’a Nusrat al-Islam wa al-Muslimin sun kai mummunan hari a Bamako babban birnin ƙasar Mali Ranar Talatar da ta gabata, 17 ga Satumba, 2024.
Wannan mummunan hari dai shine na farko da mayakan da ke ikirarin jihadi suka kai tun bayan da soja suka karɓi mulkin ƙasar a shekarar 2020.
Tuni dai Kungiyar Jama’a Nusrat al-Islam wa al-Muslimin ta dauki alhakin kai hare-hare a cibiyar horar da Jandarma da wasu sassan filin jirgin saman Modibo Keita dake Bamako a ƙasar Mali.
An kai harin ne dai a ranar da ake shirin fara sauraron shari’ar sayen jirgin shugaban ƙasa da gwamnatin da aka kifar ta yi a ƙasar Mali.
Dakarun gwamnatin Kamar Assimi sun yi alƙawarin bincikar yadda aka sayi jirgin na shugaban ƙasa a wani yunƙuri na yaƙi da cin hanci da rashawa.
A maimakon fara sauraron shari’ar da ta shafi cin hanci da rashawa, babban birnin ƙasar Mali ya wayi gari da mummunan hari daga masu iƙirarin jihadin.
A wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an hangi ɗaya daga cikin mayaƙan yana cinna wuta a jikin wani jirgin sama dake filin jirgin saman Modibo Keita