An Kama 26 Da Ake Zargin Masu Garkuwa Ga Mutane

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta kama wasu mutane 26 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, tare da ƙwato bindigogi guda 4, da muggan makamai da dama.

Ta kuma kama wani ɓangare na kuɗin fansa da ake zargin an biya masu garkuwa da mutane a wasu hari daban-daban a jihar.

Nasarar kamen dai ya biyo bayan wasu jerin samame da jami’an ’yan sanda da na ’yan banga suka yi a tsakanin ranakun 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2025, inda suka yi ta kai farmaki kan gungun masu garkuwa da mutane da ke kai hari a ƙananan hukumomin Anchau, Ikara da kuma Makarfi.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan ya fitar a ranar Alhamis, ta ce samamen da aka gudanar tare da haɗin gwiwar hukumar ’yan banga ta Kaduna, wani ɓangare ne na ƙoƙarin kawar da ’yan bindiga da yin garkuwa da mutane a jihar.

Sanarwar ta ce, an samu nasarar farko ne a ranar 5 ga watan Oktoba, a lokacin da tawagar ’yan sintiri daga reshen Anchau, da ke aikin sahihan bayanan sirri, suka kai farmaki maɓoyar wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da misalin ƙarfe 1:15 na safe, tare da kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu a ciki, ciki har da wani Jibrin Abubakar mai suna Oga, mai shekara 21.

“Bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun haɗa baki ne a ranar 22 ga watan Satumba, 2025, don yin garkuwa da wani Idris Adamu mai shekara 60, wanda suka yi garkuwa da shi na tsawon kwanaki kafin su sake shi bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan 5,” in ji Hassan.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda