Gwamnatin Kano Ta Ce Mutane 2,000 Zata Yi Wa Auren Gata

Gwamnatin Jihar Kano ta shirya gudanar da bikin ɗaura auren gata ga akalla ma’aurata dub biyu (2,000) domin ƙarfafa ɗa’a da walwalar al’umma a fadin jihar.

Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisba ta jihar Kano, Dr. Mujahiddin Aminudeen, ne ya tabbatar da hakan yayin zantawarsa da jaridar PUNCH a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa shirin na nufin rage aikata laifuka da tallafawa marasa galihu musamman zawarawa da mata da kuma waɗanda ke son aure amma ba su da hali.

Ya ce, duk ma’auratan da ke son shiga cikin shirin za su yi rajista da hukumar Hisba tare da yin gwaje-gwajen lafiya kamar na cuta mai karya garkuwar jiki da ciwon hanta, da gwajin jini domin tabbatar da lafiyarsu kafin a ɗaura musu aure.

Gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 2.5 a cikin kasafin kuɗin shekara ta 2025 domin aiwatar da wannan shiri, a matsayin wani ɓangare na manufarta ta tallafa wa al’umma da kuma tabbatar da ingantacciyar rayuwa mai ɗa’a a Kano.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda